Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Hatsarin dai ya faru ne a lokacin da tsohon shugaban kasar ta Nigeria yake kan hanyarsa ta barin filin saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe zuwa masaukinsa da ke cikin babban birnin tarayyar kasar, Abuja.
Mai Magana da yawun hukumar ta ( FRSC) Bisi Kazeem ya ce, baya ga wasu hadiman na tsohon shugaban kasar da su ka rasa rayukansu, wasu kuma an kwantar da su zuwa a asibiti saboda raunuka mabanbanta da su ka samu.
An ga tsohon shugaban kasar ta Nigeria a asibiti na wani dan lokaci, inda daga baya ya nufi masaukinsa.
342/